Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Rundunar ’yan sandan Najeriya shiyya ta ɗaya da ke Kano ta kama wani mutum mai suna Ali Alhassan Mohammed, wanda aka fi sani da Faragai, bisa zargin damfarar masu neman aikin gwamnati, kwaikwayon jami’in gwamnati da kuma jabun takardun ɗaukar aiki.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Hussaini, ya ce an kama mutumin ne bayan samun korafe-korafe daga wasu mutane da suka zarge shi da karɓar kuɗi da sunan zai samo musu aikin gwamnati.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya riƙa gabatar da kansa a matsayin mataimaki na musamman a hukumar SUBEB ta Kano, inda ya yi amfani da wannan matsayi wajen yaudarar masu neman aiki.

’Yan sanda sun ce ya karɓi sama da Naira miliyan 40 daga waɗanda ya damfara, yayin da fiye da mutane 20 suka ce ya yaudare su.

Haka kuma, an gano cewa ya ƙirƙira tare da rarraba jabun takardun ɗaukar aiki ga wasu daga cikin waɗanda ya karɓi kuɗinsu.

An kwato wasu daga cikin takardun jabun a matsayin hujja, kuma wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu.

Rundunar ta gargadi jama’a da su yi hattara da masu neman kuɗi da sunan samo aikin gwamnati, tare da tabbatar da irin waɗannan tayin ta hanyoyin hukuma.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.