Ba Gaskiya Ba Ne Cewa Atiku Zai Jingine Siyasa – Melaye

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma DINO MELAYE  ya mayar da martani kan ikirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na shirin yin ritaya daga siyasa.

Melaye ya ce maganar cewa Atiku zai yi ritaya daga siyasa ya hada hannu da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu karya ce.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin yakin neman zaben Atiku da Okowa, ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba mai rike da tutar jam’iyyar PDP zai dawo kan sharafinsa.

Atiku ya zo na biyu a zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sai dai ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben da aka yi.

Tuni dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu.

Post masu alaƙa

Dalibai huɗu za su wakilci Najeriya a gasar Spelling Bee ta Duniya a China

Babandede Ya Taya Shettima Murnar Sake Samun Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

Ban taɓa haɗuwa da Adeyemi ba — Gbajabiamila