Jihar Neja: Wasu Mutane 11 Sun Rasa Rayukansu a Wani Haɗarin Mota

Kasa da sa’o’i 24 da rasa rayukan mutane 11 a hanyar Mokwa zuwa Lapai a Jihar Neja, wasu mutane 24 sun mutu a wani hatsarin mota da auku a hanyar Kutigi zuwa Bida a jihar.

Wani ganau ya shaida wa MUHASA  cewa hatsarin ya auku ne da tsakar daren ranar Talata a kauyen Etsuworo, inda wata babbar mota ta taso daga Zariya zuwa Jihar Legas.

Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa mutane 24 ne suka mutu a hatsarin, kuma an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kutigi, da ke hedikwatar karamar hukumar Lavun ta jihar.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.