Sarkin Kano Ya Jajanta Wa ‘Yan Kasuwar Singa

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa ‘ƴan kasuwar Singa bisa iftila’in gobara da ta tashi a kasuwar SHEKARAN JIYA.

Sarkin ya jajanta wa ƴan kasuwar ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar yau.

Sanarwar ta ce, “Mai Martaba Sarki ya nuna damuwarsa matuka a lokacin da ya samu labarin tashin Gobarar”.

Haka kuma a cikin sanarwar, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa ‘ƴan Kasuwar Kurmi da ta Rimi waɗanda su ma suka gamu da ifila’in gobara kwanakin baya.

Mai martaba Sarkin ya buƙaci ƴan kasuwar har ma da ƙungiyoyinsu da su ci gaba da yawaita yin adduo’o’i tare da ɗaukar matakan kare afkuwar irin wannan iftila’i a nan gaba.

Post masu alaƙa

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da rumbum abinci ga jama’ar kudu maso kudancin Najeriya.