Sarkin Musulmi III ya buƙaci ƙungiyar ƙwadago ta janye shiga yajin aiki

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli a Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su janye batun yajin aiki da zasu shiga a faɗin ƙasar daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba.

Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen bude taron shirya bikin cikar ƙasar nan shekaru 63 da samun ‘yancin kai wanda ya gudana a jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja.

Ya jaddada buƙatar tattaunawa don nemo mafita kan batutuwan maimakon fara yajin aikin ko don maslahar talakawa.

A ƙarshe ya ce yana mai bayar da shawarar tattaunawa ne saboda yajin aikin ba zai magance matsalolin ƙasar nan ba.

Post masu alaƙa

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.