Sashen Lura da Basussukan Najeriya, DMO, ya ja hankalin shugaba Tinubu game da ciwo bashi

Sashin lura da al’amuran bashi a Najeriya DMO, ya gargadi gwamnatin tarayya game da ƙarin karbo aron kudi a irin halin da ake ciki.

 Inda ya ce, an fadawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama dole ya gujewa cin bashi a yanzu.

Hukumar ba ta goyon bayan cin bashin ganin cewa kashi 73.5  na kudin shigar da za a samu a bana duk zai tafi ne a wajen biyan bashin da aka karbo.

Haka zalika hukumar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemi hanyoyin da za tayi wajen ganin ta kara samun kudin shiga a cikin lalitar ƙasar nan.

Post masu alaƙa

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da rumbum abinci ga jama’ar kudu maso kudancin Najeriya.