Sheikh Fethullah Gulen Ya Rasu Yana Da Shekaru 83

Malamin addini kuma babban ɗan Adawa ga shugaba Racep Tayyib Erdagon a ƙasar Turkiyya Fethullah Gulan ya rasu yana da shekaru 83 bayan rashin lafiya a kasar Amurka.

An an zargi Sheikh Gulan a baya da kitsa juyin mulkin da baiyi nasara ba ga Racep Tayyib Erdagon a shekarar 2016.

Marigayin Malamin ne dai ya samar da ƙungiyar International Islamic Movement kuma na hannun daman shugaba Erdagon kafin a zarge shi da kitsa juyin mulki ga Shugaban.

Sheikh Gulen ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti dake ƙasar Amurka, kuma ya yi zaman neman mafaka na sa kai a ƙasar tun shekarar 1999.

Duk da ba’a bayyana musabbabin mutuwar ta sa ba, rahotanni daga makusantansa sun bayyana cewa an kwantar dashi ne asibitin saboda matsalar ciwon ƙoda.

A lokacin da yake jagorantar ƙungiyar siyasa a musulunci a ƙasar, Shugaba Erdagon ya yi amfani da wasu mabiyan sa kuma sun sami muƙamai a gwamnatin sa.

Sai dai a shekarar 2016 ne manyan abokan suka juye zuwa abokan hamayya, inda gwamantin Turkiyya ta ayyana ƙungiyar Sheikh Gulen a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.