Gwamnonin Arewa Sun Tallafawa Jihar Jigawa Da Naira Miliyan 950

Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta bayar da gudunmawar Naira Miliyan 950 don taimakawa iyalan waɗanda suka rasu dama waɗan da suka jikkata sakamakon faɗuwar tankar dakon man fetur a Majia jihar Jigawa.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ne ya sanar da ba da tallafin ya yin ziyarar da su ka kai don Jajantawa gwamnati dama al’ummar Jihar.

Jama’a daga da wajen Najeriya na cigaba da jajantawa al’ummar jihar Jigawa faruwar wannan ifti’ai.

A kwanakin baya ma dai al’ummar ƙauyen Nahuche da ke ƙaramar Hukumar Taura sun fuskanci ifti’ain ambaliyar ruwa da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

  • Jihar Jigawa na ɗaya daga cikin jihohin da ke da zaman lafiya a Arewacin Najeriya, sai dai a bana an samu mace-mace da dama sakamakon ifti’ai iri daban-daban.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.