Shettima Ya Fasa Zuwa Taron Ƙungiyar Ƙasashen Rainon Ingila

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya fasa zuwa taron da ƙungiyar ƙasashe rainon Ingila ta Commonwealth na shekarar 2024, da za’a gudanar a tsibirin Samoa.

Shettima ya fasa zuwa taron ne saboda matsalar da jirgin sa ya samu a lokacin da ya yada zango a ƙasar Amurka.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya ce a lokacin da jirgin ya yada zango a birnin New York, wani abu ya daki jirgin mataimakin shugaban kasar wanda yayi sanadiyyar lalata gilas ɗin direban jirgin.

Sanarwar ta ƙara da cewa tuni dai Shugaba Tinubu ya amince da tura tawagar ministoci, ƙarƙashin jagorancin ministan Muhalli, Abbas Lawal domin su wakilci Najeriya.

Tun ranar 21 ga watan Oktoba, aka fara taron inda za’a gama shi a ranar 26 ga watan Oktoba a tsibirin da ke tekun Pacific.

An dai fara taron ne ranar 21 ga watan Oktoba, wanda kuma ake sa ran kammala shi ranar 26 ga watan Oktoba a tsibirin da ke tekun Pacific.

Tuni dai tawagar mataimakin shugaban kasar suka kamo hanyar su zuwa gida Najeriya

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda