Home » Shugaba Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Kai Ziyarar Aiki Saudiyya

Shugaba Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Kai Ziyarar Aiki Saudiyya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Abuja, Babban Birnin Tarayya bayan ya shafe kwanaki takwas yana ziyarar aiki a kasar Saudiyya.

Buhari ya yi Umarah a yayin Ziyarar wadda fadar tasa ta ce ita ce ta karshe, kafin karewar wa’adin mulkinsa,.

Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu, wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da maraicen jiya Laraba, ya ce Buhari ya sauka a Abuja da misalin karfe 5:08 na yamma.

Sai dai Garba Shehu ya ce sai da jirgin Buhari ya shafe kusan awa bakwai kafin ya iso Najeriya saboda sai da ya kaurace wa bi ta kasar Sudan wacce a halin yanzu take fama da rikici.

Ya ce sai da jirgin da ya taso daga birnin Jiddah ya bi ta kasashen Eritrea da Habasha da Kenya da Uganda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sannan ya bi ta Kamaru kafin daga karshe ya iso Najeriya.

Bayan isar tasa a filin jirgin sama na Abuja, Buhari ya sami tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Danmallam Mohammed wanda ya wakilci Babban Sufeton da kuma Shugaban Hukumar Tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?