Shugaba Tinubu ya ba da umarnin sake nazarin ba da tallafin Naira 8,000

Biyo bayan cece-kuce da suka da jama’a ke ta faman yi, gwamnatin Tinubu ta umurci sake nazarin shirin bayar da tallafin kudi na Naira 8,000 da nufin samar da agaji ga magidanta masu karamin karfi don rage radadin cire tallafin man fetur.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake a wata sanarwa da ya fitar ya ce, gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar fifita bukatar ‘yan Nijeriya da jin dadinsu da tsaronsu fiye da bukatarta a karkashin shirin “Sabunta kwarin guiwa”, wanda hakan ya sanya daukar matakin gaggawa.

Sai dai shirin ya gamu da cece-kuce da suka, inda jama’a da dama ke nuna rashin jin dadi da kuma shakku kan tasiri da ingancin shirin.

Shugaba Tinubu ya bada muhimmanci kan ra’ayoyin jama’a, inda ya bada umarnin sake nazarin shirin bayar da tallafin cikin gaggawa.

Post masu alaƙa

Manjo Janar Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Yan Bindiga

JIBWIS Gwallaga Sun Ziyarci A Sansanin Alhazai Na Jihar Bauchi Domin Bada Agaji

‘Yan Arewa A Jihohin Kudu Sun Koka kan Tsangwama da Wariya Saboda Matsalolin Tsaro