Majalisar dokokin Kano ta jingine tuhumar da take wa tsohon mataimakin gwamna Aminu Abdussalam

Majalisar dokokin jihar Kano tace ta janye tuhume tuhumen da take yiwa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, biyo bayan ajiye mukamin sa na Mataimakin Gwamna Jahar Kano

Majalisar ta bayyana hakan ne a zaman ta na yau karkashin Jagorancin Rt Hon Jibrin Isma’il Falgore.

Da yake ƙarin haske dangane da lamarin, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin, Hon Lawan Husaini Cediyar Yan’gurasa ya ce , yanzu majalisar bata da wani hurumi akan batun tuhumar da take yiwa tsohon mataimakin gwamnan

“Dama iya hurumin mu shi ne muyi bincike idan an same shi da laifi mu tsige shi daga mukamin sa,to sai gashi ya sauka tun kafin ma mu kammala, don haka yanzu bamu da wani hurumi tun da mu ba yan sanda ba ne”

Kazalika majalisar ta Amince da ritayar mataimakin gwamna a hukumance, yayin zaman majalisar na yau dan’majalisa mai wakiltar karamar hukumar ,Ƙiru Hon Usman Tasi’u, ya sanarwa da majalisar cewa ya fice daga jam’iyyar NNPP  zuwa ADC

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda