Shugaban Najeriya Ya Nada Sabuwar Babbar Akanta Janar Ta Ƙasa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nada Oluwatoyin Madein a matsayin sabuwar Babbar Akanta Janar.

Wata sanarwa da Darektan sadarwa a ofishin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Mohammad Abdullahi Ahmed ya fitar a ranar Juma’a ce ta sanar da nadin Oluwatoyin.

Shuagbar Ma’aikatan Gwamnati Tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan ce ta sanar da nadin Dr. (Mrs.) Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin Babbar Akanta Janar, bayan da aka bi matakan tantancewa don cike gurbin.

Wannan nadi ya fara aiki nan take daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayun 2023. Sanarwar ta ce.

Kafin nada ta a wannan mukami, Oluwatoyin ta kasance Darektar Kudi a Ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr