Wata Jiha a Amurka Ta Haramta ‘Yan Jihar Amfani da Manhajar TikTok

Gwamnan jihar Montana, Greg Gianforte a ranar Laraba ya rattaba hannu kan wata doka ta haramta amfani da Manhajar TikTok mallakar kasar China a jihar.

Montana za ta haramtawa rumbun Google da Apple damar sauke manhajar TikTok a cikin jihar, amma ba za ta zartar da wani hukunci ga daidaikun mutane masu amfani da app din ba. Haramcin zai fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2024.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin TikTok ya fitar yana mai kalubalantar dokar, ya ce “wannan sabuwar dokar ta taka hakkin mutanen Montana ta hanyar dakatar da amfani da Manhajar TikTok ba bisa ka’ida ba.

“Don haka, za mu cigaba da wanzar da ayyukanmu aciki da wajen Montana don kare hakkin masu amfani da Manhajar mu”

TikTok, yana da mabiya a Amurka mutum sama da miliyan 150, manhajar tana fuskantar kalubalen kiraye-kiraye daga ‘yan majalisar dokokin Amurka da gwamnonin jihohin kasar da a haramta manhajar a duk fadin kasar sabida damuwa game da yuwuwar tasirin gwamnatin China kan manhajar.

Post masu alaƙa

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.

Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da rumbum abinci ga jama’ar kudu maso kudancin Najeriya.