Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yaba wa Farfesa Ali Pate, ɗaya daga cikin ministocin da majalisr dattawa ta amince da su, bisa kwazon da ya nuna a lokacin da ake tantance shi a majalisar.
Farfesa Pate ya taɓa riƙe muƙamin ƙaramin ministan lafiya a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.
Kafin a naɗa shi ya zama minista, Pate ya yi murabus daga shugabancin kamfanin ‘GAVI- Global Alliance for Vaccines and Immunization’ inda ya yi nuni da cewa zai samu muƙami a gwamnatin Shugaba Tinubu.
A jiya Talata, 8 ga watan da muke ciki, Pate ya raka Ngozi Okonjo-Iweala, Darekta Janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya domin ziyartar Shugaba Tinubu a fadarsa.
Shugaba Tinubu ya gaya masa cewa ya kalli yadda tantancewar ta sa ta kasance a talbijin ya kuma yaba masa da irin ƙwazon da ya nuna a wajan.