Shugabannin Turai sun yi wa Trump tawaye kan yaƙin Iran

Karin wasu shugabannin Turai sun yi watsi da buƙatar Shugaban Amurka Donald Trump ta neman taimako wajen tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz, da Iran ta rufe.

Bayan wani taron ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai, babbar jami’ar kula da manufofin ƙasashen waje ƙungiyar, Kaja Kallas, ta ce “babu wanda ke son yin hakan” inda ta kara da cewa ”Wannan ba yaƙi ne na ƙasashen Turai ba”.

Shi ma shugaban Finland, Alexander Stubb, ya shaida wa BBC cewa Mista Trump ne da kanshi ya yanke shawarar ƙaddamar da yaƙi kan Iran ba tare da shawarar kowa ba, don haka kamata ya yi ya lalubo bakin zaren warware matsalar da ƙashin kansa.

Wakilin BBC ya ce shi ma shugaban gwamnatin Jamus Friedrick Merz, ya ce yaƙin na Iran, ba batu ne da ya shafi NATO ba, yayin da mahukunta a Paris, suka fito ƙarara, suka shaida wa Trump cewa ba za su aika dakarunsu mashigin Hormuz ba.

Tun da farko a Fadar White House, Shugaba Trump ya sake ragargazar kasashen duniya, da ya ce sun ja baki sun yi shiru a kan shirin nasa.

Post masu alaƙa

Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari