• Home  
  • Mutanen Da AmbaAliyar Ruwa Ta Kashe A Neja Sun Kai 110
- Babban Labari - Labarai

Mutanen Da AmbaAliyar Ruwa Ta Kashe A Neja Sun Kai 110

Alkaluman waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a jihar Neja ya kai mutum 110, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa na jihar. Masu aikin ceto sun ce sun gano gawawwaki da dama. Jami’ai a yankin Mokwa wurin da lamarin ya faru, sun yi gargaɗin cewa ƙarin mutane na cikin barazana a birnin. An shafe tsawon […]

Alkaluman waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a jihar Neja ya kai mutum 110, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa na jihar.

Masu aikin ceto sun ce sun gano gawawwaki da dama.

Jami’ai a yankin Mokwa wurin da lamarin ya faru, sun yi gargaɗin cewa ƙarin mutane na cikin barazana a birnin.

An shafe tsawon sa’o’i ana tafka mamakon ruwan sama a yankin ranar Laraba, inda ruwa ya tafi da gidaje aƙalla 50.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin yiwuwar samun ambaliya a kusan rabin jihohin ƙasar 36.

Sama da mutum 1,200 ne suka mutu sakamakon ambaliya a bara sannan sama da miliyan ɗaya suka ɗaiɗaita, a ambaliyar da ba a taɓa gani ba cikin gomman shekaru.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai