Sojojin Isra’ila Sun Saɓa Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Lebanon 

Kamfanin Dillancin Labaran Lebanon NNA ya bayyana cewa sojojin Isra’ila sun saɓa ƙa’idar yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙasarsu ta shiga.

NNA ya tabbatar da cewa zuwa yanzu sojojin Isra’ila sun saɓa yarjejeniyar sau bakwai, ciki har da harbi a ƙauyukan da ke kudancin Lebanon.

Rahotanni na cewa saɓa yarjejeniyar ta fi faruwa ne a gundumar Marjayoun ƙarƙashin yankin Nabatieh da kuma gundumar Tyre.

An ga wata tankar yaƙin Isra’ila ta harba bam wani gida a yankin Tel Nahas kusa da Burj Al-Moulouk, inda mai gidan ya tsallake rijiya da baya.

An ce sojojin sun kuma harba bama-bamai garuruwan Markaba da Talloussa da Odaisseh da Taybeh da kuma Houla, sannan sun tura tankokin yaƙi huɗu zuwa yammacin Khiyam.

Daga cikin saɓa yarjejeniyar da aka shiga, A Khiyam, an ba da rahoton cewa sojojin Isra’ila sun buɗe wuta kan wasu mutane da ke tafiya hanyar zuwa jana’izar wasu da aka hallaka.

Post masu alaƙa

Tinubu Ya Sha Alwashin Ceto Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Oyo Da Borno

Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP I.A. Bakori ya gargaɗi dakarunsa su guji shiga harkokin siyasa.

Alhazan Kebbi Rukunin Farko Sun Dawo Gida