An Zaɓi Alhaji Muhammad Babandede OFR Shugaban Majalisar Zartarwar NBMOA

Mamallakin tashoshin rediyo da talabijin na MUHASA Alhaji Muhammad Babandede OFR, ya zama Shugaban Majalisar Zartarwar Kungiyar Masu Gidajen Rediyo Da Talabijin Masu Zaman Kansu Na Arewacin Najeriya. 

Wannan zaɓe na ƙunshe a cikin wata takarda ta musamman da Shugaban Majalisar Amintattu na ƙungiyar Alhaji Dokta Ahmed Tijjani Ramalan ya sanya wa hannu.

Shugaban Majalisar Amintattun ƙungiyar ta NBMOA ya ce Alhaji Muhammad Babandede OFR zai riƙe wannan muƙami ne an tsawon watanni 6.

Inda ake sa ran a zamansa na shugabancin wannan ƙungiya zai gudanar da zaɓen cike guraben da ake da su.

Dokta Ramalan ya ce suna sa ran gogewar Alhaji Muhammad Babandede zai taimakawa ƙungiyar zuwa tudun mun tsira.

Ya kuma bayyana cewa suna da yaƙinin Alhaji Babandede zai samarwa ƙungiyar ‘yanci da mutunci a idon duniya.

Takardar ta bayyana cewa Alhaji Muhammad Babandede OFR zai shiga ofishinsa a matsayin shugaban majalisar zartarwar ƙungiyar daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.

 

Post masu alaƙa

Mace ta farko ta fito neman takarar gwamnan Gombe a APC a zaɓen 2027.

Saudiyya Ta Ba Ɗaliban Najeriya 50 Guraben Karatu A Fannin Man Fetur Da Ma’adinai

Shugaba Tinubu ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027