Da sunan Allah mai girma, tsira da amincin Sa, su tabbata ga manzon Sa mai falala.
Bayan haka, yau zamu yi duba ne akan muhalli da irin matsalar dake tattare da shi.
Hakika ga duk mai yawo a biranen kasar nan, zai ga akwai matsaloli na rashin tsaftar muhalli.
Wannan ba zai rasa nasaba da cinkoson jama’a a biranan ba, da kuma kiwa da lalaci. Nace kiwa da lalaci saboda da yawa daga cikin mu muna da sakaci wajen bada kulawar da ta dace a wannan fanni.
Abu ne mai sauki ka shiga gidajen mu kaga tarin sharar da yakamata ace an fitar zuwa inda ya dace, amma an bar ta.
Sau da yawa kuma zaka ga in an fitar da ita daga gidan ma, sai a aje ta in da bai dace ba. A tsarin zamantakewa irin tamu, da kuma koyarwa irin ta musulunci, tsafta abace muhimmiya. Amma sai gashi muna sakaci wajen kulawa da ita.
Yanzu ka dauki titunan mu manya da kanana, sai kaga an debo shara daga gidaje ko kasuwanni an jibge. Masu wannan sukan fake da cewa ai motocin hukumar debe shara zasu zo su debe.
Su kan manta da cewa harkar kula da muhalli abu ne da ya shafi kowa. Maimakon a dinga aje shara a tituna, zai fi kyau a samu wuri a cikin unguwa ko kasuwa a tara, yadda in motocin kwashe sharar sun zo sai su debe.
Na kan ji takaici sau da dama, in naga tarin shara bisa tsakiya ko gefen titi. Domin hakan na jawo cinkoson ababen hawa tare da jinkirtar da zirga-zirgar jama’a.
Duk da cewa akwai shirin tsaftar muhalli na wata-wata wanda jihohi da dama suke yi. Hakan bai hana biranen mu zama da tarin shara barkatai ba. Wani karin takaicin shine yanda wadansu ke amfani da wajajen da ake zube sharar a matsayin wajen tsugunno. Sai kawai kaga mutum ya tsuguna a kai ko gefen shara yana bahaya. Dalilin sa ai wajen aje shara ne. wanda hakan yake sanadin yaduwar cutuka musamman kwalara. Ko a yan’watannin baya an yi fama da cutar kwalara, wanda har rashe-rashe an samu.
A rahoton kwamitin muhalli na majalisar dinkin duniya da aka fitar a yan’kwanakin nan, kasashen Najeriya da Indiya suke kan gaba wajen wannan matsala ta yin bayan gida a fili barkatai.
Lalle zai yi kyau mu lura da tsaftar muhallin mu, ta hanyar tara shara da aje ta a inda ya dace. Mu kiyayi aje ta ko ina don tsare yaduwar cutuka.
Haka kuma kira ga hukumomin kula da tsabtar muhalli, shine su dada himma wajen gabatar da aikin su. Sau da yawa zaka ga an bar shara tsawon lokaci a tsakiyar manyan tituna ko gefe, ba a debe ba. Wani lokacin kuma kaga ana aikin debewar da rana, lokacin da mutane suke harkokin neman su. Sai kaga duk an takura. Shawara ta ita ce in zai yiwu a maida aikin da dare (matukar hakan bai da wata cutarwar).
Daga Muhammad S. Ahmad
Bayero University Kano
28/ 11/ 24