­­­Sojojin Sudan Sun Yanye Daga Yarjejeniyar Tsagaita Wuta da RSF

Jami’an gwamnatin Sudan sun ce sojojin kasar sun dakatar da tattaunawar dakatar da bude wuta da dakarun kar-ta-kwana na RSF, inda suke zargin ƴan kungiyar da saba yarjejeniyar akai-akai.

Haka kuma wani jami’in diflomasiyya na Sudan sun bayyana wa Reuters, cewa batun janyewar sojojin na Sudan daga tattaunawar yarjejeniyar wadda ake kokarin tabbatarwa domin bayar da damar kai kayan agaji ga wadanda suke matukar bukata

A ranar Litinin masu shiga tsakani daga Saudiyya da Amurka suka ce sojojin da RSF sun amince su tsawaita yarjejeniyar da kwana biyar.

Sai dai kuma an ci gaba da fada a sassa daban-daban na kasar ciki har da babban birnin kasar Khartoum, inda RSf ta ce an kai wa inda dakarunta suke hari.

Post masu alaƙa

‘Yan Arewa A Jihohin Kudu Sun Koka kan Tsangwama da Wariya Saboda Matsalolin Tsaro

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama