Za mu fara kamen fasinjojin ‘yan achaɓa a Abuja ~ Nyesom Wike
Hukumar Raya Birnin Abuja ta bayyana cewa za ta fara kamen fasinjojin dake hawa achaba. Hukumar wadda ke karkashin jagorancin ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce idan ta kama fasinjoji masu hawa achaba dole a bar yin sana’ar a birnin.



