Tag: Abuja

Babban Labari Labarai

Gwamnati ta maka El-Rufai a Kotu

Gwamnatin Tarayya ta maka Nasir El-Rufai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a kotu, kan zargin kutsen intanet a layin sadarwar Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu. Hukumar Tsaro ta DSS ce ta shigar da kara gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda take tuhumar El-Rufai da laifuka uku masu alaka da kutsen intanet. […]

Babban Labari Labarai

Ana zanga-zanga kan dokar gyaran zaɓe a Najeriya

An fara zanga-zanga a Abuja, babban birnin tarayya, yayin da jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin kwadago ke zargin Majalisar Tarayya da tauye dimokuraɗiyya ta hanyar ƙin amincewa da ƙudirin da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura. Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da ‘yan majalisa suka ƙi amincewa da wani sashe na […]

Babban Labari Labarai

Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma aiki

Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci ma’aikatan Abuja su koma bakin aiki bayan cimma matsaya da ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, biyo bayan taron sulhu da aka gudanar domin warware matsalolin da suka haifar da yajin aikin da ake yi. Taron ya gudana bisa jagorancin shugaban kwamitin majalisar dattawa na Abuja, Sanata Mohammed Bomoi. Sanarwar […]

Babban Labari Labarai

Kotu ta ba Yahaya Bello damar tafiya Umara a watan azumi

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, izinin tafiya Saudiyya domin yin Umara a kwanaki 10 na watan Ramadan mai kamawa. A yayin zaman kotun na ranar Alhamis, alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin a saki fasfo ɗin tafiya na tsohon gwamnan, wanda yake a […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000