‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Budurwa Daga Hannun Matsafa A Abuja
Rundunar ‘Yan Sanda a babban birnin tarayya Abuja, ta sami nasarar gano wata budurwa da wasu da ake zargin Matsafa ne suka tsafeta a dakin Otal.
Rundunar ‘Yan Sanda a babban birnin tarayya Abuja, ta sami nasarar gano wata budurwa da wasu da ake zargin Matsafa ne suka tsafeta a dakin Otal.
Kamfanin Dillancin Wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya ce ɓarayi sun sake lalata layinta mai karfin Volt 132 (KV) da wayoyin karkashin kasa a Abuja.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Abuja ta kama wata mota makare da ƙananan yara har 59 da ake zargin an sato su daga Arewacin Najeriya.
Wani bam ya tashi a makarantar Islamiyya ta Sani Uthman da ke Kuchibuyi a Ƙaramar Hukumar Bwari a Abuja, inda ɗalibai biyu suka rasu, sannan wasu huɗu suka jikkata.
A ranar Litinin 28 ga Satumbar 2024 ake sa ran wa’adin da Ministan Abuja Nyesome Wike ya bai wa mabarata na su fice daga birnin zai ƙare. Kungiyar masu buƙata ta musamman dake Arewacin Najeriya ta yi kira ga ‘ya’yan ta da su tashi da azumi don neman taimakon Ubangiji bisa umarnin na ministan Abuja. […]
Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya ta ce Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) sun kai samame ofishin su da ke Abuja.
Shugabar gidan Rediyo da Talabijin na Muhasa Aishatu B.Sule wadda ta halarci taron a Abuja ce ta rubuto mana cewa an rantsar da sababbin shugabannin kungiyar Ma’aikatan Kafafen Yada Labarai wato SNB wadanda aka zaba a Abuja. An rantsar da su ne a walimar cin abincin dare a Otel din NICON LUXURY da ke birnin […]
Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya ta rikide zuwa tashin hankali, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 14 a manyan biranen kasar. Zanga-zangar dai ta samo asali ne sakamakon cire tallafin man fetur da kuma karyewar darajar Naira. Zangar-zangar da a farko aka tsara a matsayin ta lumana ta janyo asarar rayuka […]
Wata ƙungiya mai zaman kanta, ta yi kira ga masu ruwa da tsaƙi da malaman addini a Najeriya da su sa hannu kan yaƙin da ake yi wajen kawo ƙarshen safarar bil’adama a ƙasar nan.
Hukumar Raya Birnin Abuja ta bayyana cewa za ta fara kamen fasinjojin dake hawa achaba. Hukumar wadda ke karkashin jagorancin ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce idan ta kama fasinjoji masu hawa achaba dole a bar yin sana’ar a birnin.