Labarai
Hatsarin Kwale-Kwale Ya Yi Sanadin Rasa Rayuka A Adamawa
An tabbatar da mutuwar mutane takwas a Rugange da ke ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, a jihar Adamawa, sanadiyar kifewar kwale-kwale a ƙarshen makon nan, kuma wasu mutane 15 sun ɓace a ruwa ba a gan su ba.

