A yau Talata Ake Jiran Isowar Shugaban Kasar Najeriya, Tinubu, daga kasar waje
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Tinubu wanda ya bar kasar a ranar 20 ga watan Yuni zuwa birnin Paris na da niyyar komawa Najeriya don yin bukin babbar Sallah a gida.