Wasu tsuntsaye masu Jan baki sun afkawa gonakin noman shinkafa a jihar Kebbi

Aƙalla mutum 100 ne suka rasa gonakinsu yayin da dandazon tsuntsaye jan-baki suka afka wa gonakin shinkafa a garin Argungu na jihar Kebbi.

Mazauna yankin sun ce tsuntsayen sun lalata kusan hekta 75,000 na gonankin a ranakun ƙarshen makon nan.

Sun ƙara da cewa “Bayan matsalolin da muke ciki na tsadar man fetur da taki, ga kuma tsuntsaye.

Mutum bai isa ya zauna a gida ba, in ba haka ba kuma za su lalata gonarsa baki ɗayanta,” Wani manomin min ma ya ce ya shafe shekara 20 yana noman shinkafa amma bai taɓa ganin irin wannan bala’i ba.

Ba wannan ne karon farko da ake samun hare-haren tsuntsayen ba amma wannan ne mafi muni a baya-bayan nan.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr