Nigeria

EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta tsare tsohon ministan ƙwadago kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Chris Ngige. Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe, ya tabbatar da tsare shi da safiyar ranar Alhamis, bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewa an sace shi. Chukwuelobe ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige […]

Read more

Amurka ta yaba da ceto ɗaliban jihar Neja 100

Amurka ta yaba wa gwamnatin Najeriya kan ceto wasu daga cikin ɗaliba 100 na makarantar St Marys da aka sace a Papiri da ke jihar Neja, tana mai cewa hakan na nuna sabon kuzari da jajircewar gwamnati wajen tunkarar matsalolin tsaro. Jami’in Amurka Riley Moore ne ya bayyana haka cikin wani saƙon godiya da ya […]

Read more

Senata Ndume ya buƙaci Tinubu ya janye sunayen jakadu

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ke gaban majalisar a halin yanzu, bisa zargin cewa an saba wa ƙa’idar tsarin tarayya da kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada. A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne majalisar […]

Read more