Matawalle Ya Isa Birnin Kebbi Bisa Umurnin Tinubu

Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya isa tashar jirgin sama ta Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, domin taimaka wa da sa ido kan yunƙurin ceton ɗaliban da aka sace a jihar ta Kebbi.

A ranar alhamis ne Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi ya koma jihar – da ke arewa maso yammacin Najeriya – har sai an dawo da ɗaliban gida.

A farkon wannan mako ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga makarantar Sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar tare da sace ɗalibai 25.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.