Tag: Nigeria

Babban Labari

Tinubu ya gana da shugaban Chadi

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙucnin shugaban Chadi Idriss Déby a ranar Alhamis. Sun yi ganawar ce cikin sirri a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja, inda ake sa ran sun tattauna kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da kuma haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Ganawar na zuwa ne kafin tafiyar shugaba […]

Babban Labari

Harin Iran ya jikkata sojojin Amurka 12 a Saudiyya

Rahotanni sun ce wani harin makami mai linzami daga Iran ya jikkata sojojin Amurka 12 a wani sansanin soji da ke Saudiyya. Jami’ai sun shaida wa abokiyar hulɗar BBC, wato CBS, cewa wasu daga cikin sojojin sun samu munanan raunuka a sansanin jiragen sama na Yarima Sultan. Harin ya kuma lalata wasu jiragen sojin saman […]

Babban Labari

Mahaifiyar Nasir El-Rufai ta rasu

Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai mai suna Hajiya Umma El-rufai ta rasu. Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne ya sanar da rasuwar a ranar Juma’a, inda ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ina sanar da al’umma cewa Allah ya yi wa kakata, Hajiya Umma El-Rufai […]

Babban Labari Labarai

A gaggauta sakin ’yan Najeriya 42 da aka kama a Mozambique — NiDCOM

Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta buƙaci mahukuntan ƙasar Mozambique su gaggauta sakin ’yan Najeriya 42 da aka kama a ƙasar ba tare da bayyana takamaiman laifin da suka aikata ba. Shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana damuwa kan lamarin, tana mai cewa kama ’yan Najeriya ba tare da tuhuma ba abin takaici […]

Babban Labari Labarai

Kamfanin Maltina yasha alwashin samarwa mutane 20,000 aiki nan da shekarar 2030 a Nijeriya.

Kamfanin Maltina ya bayyana cewa zai samar da ayyukan yi ga manoma sama da 20,000 a jihar Jigawa nan da shekarar 2030, a wani sabon shiri da kamfanin ya ƙaddamar domin bunƙasa noman sha’ir (Maltina Barley Field Day) da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’umma. Shirin, wanda aka ƙaddamar da nufin tallafa wa manoma su rungumi noman zamani, […]

Babban Labari Labarai

Sai ƴan Arewacin Nijeriya sun daina yi wa kansu hassada za a samu ci gaba- Alhaji Shehu Ashaka.

An bayyana rashin haɗin kai tsakanin al’ummar arewacin Nijeriya amatsayin abin da ke ƙara janyo wa yankin koma baya ta fuskar ci gaba da kuma rusa zamankewarsu. Dattijo a arewacin Nijeriya kuma ɗan kasuwa, Alhaji Shehu Ashaka, ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da gidan telebijin da Radiyo na Muhasa. Alhaji Shehu Ashaka, wanda […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000