Tag: Nigeria

Labarai

Najeriya ta soki harin da Houthi ta kai wa Saudiyya

Najeriya ta yi Allah-wadau da harin da mayaƙan Houthi suka kai filin jirgin saman King Khalid da ke Riyad babban birnin Saudiyya. Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriyan ta fitar a yau, ta ce harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 12 tare da jikkata sama da 300 abin Allah wadai ne. Sanarwar […]

Labarai Siyasa

Bai kamata ’yan Najeriya suke shan wahala haka ba — Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a Najeriya. A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku, ya ce gwamnati ta gaza kare ’yan Najeriya daga matsananciyar […]

Labarai

Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi zuwa shekarar 2060.

Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi da rage hayakin da ke haddasa ɗumamar yanayi zuwa shekarar 2060. Mai ba shugaban ƙasa shawara a Ofishin mataimakin Shugaban Ƙasa kan ayyukan raya ƙasa, Hon. Musaddiq Mustapha Adamu, ya ce kuɗaɗen za su taimaka wajen samar da makamashi mai tsafta da […]

Babban Labari

Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau – Shettima

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƙasar ta tsallake wani muhimmin mataki a sauye-sauyen tattalin arzikinta, kuma yanzu tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa. Bayanin na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar. Shettima ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa sun […]

Labarai

An dakatar da shugaban NSCDC a Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adanai 37

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin dakatar da shugaba hukumar tabbatar da tsaro da kare haƙƙin al’umma, NSCDC a jihar Neja, Suberu Aniviye, sakamakon mutuwar wasu matasa da ake zargin masu haƙar ma’adanai ne ta ɓarauniyar hanya. Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayar da umarnin a sanarwar da ya wallafa a shafinsa […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai