Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.
Rundunar ’yan sandan Najeriya shiyya ta ɗaya da ke Kano ta kama wani mutum mai suna Ali Alhassan Mohammed, wanda aka fi sani da Faragai, bisa zargin damfarar masu neman aikin gwamnati, kwaikwayon jami’in gwamnati da kuma jabun takardun ɗaukar aiki. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Hussaini, ya ce an kama mutumin […]