Rundunar yan sandan jihar Kano ta lashi Takobin hana masu yunkurin aikata laifuka sakat.

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta lashi takobin kara zage damtse na dakile aikata laifuka, a sassan jihar baki daya.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan, yayin bikin karin girma ga wasu jami’an yan sanda 13.

Kwamishinan yan sandan ya taya wadanda suka samu karin girman murna, tare da jan kunnensu su kara zage damtse na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyin su.

CP Bakori, ya kara da cewa, a matsayin sun a jami’an yan sanda sun kara damara wajen dakile miyagun aiyuka don haka duk wanda yake da burin shigowa jihar, don aikata laifi su san cewa basu da wajen zama a fadin jihar.

Ya kuma yi kira ga mutanen gari su ci gaba da taimaka musu wajen basu bayan sirri don magance matsalar tsaron musamman yunkurin yan bindiga daga jihar Katsina.

Haka zalika ya godewa gwamnatin Kano, bisa hadin kai da goyon bayan da suke bawa hukumomin tsaron jihar, don tabbatuwar zaman lafiya.

Wadanda suka samu karin sun hada da mukaddashin kwamishinan yan sanda 1 ( DCP), mataimakan kwamishinan yan sanda 4 (ACP), CSP 7 da kuma SP 1.

Kwamishinan ya ce sun shiga dazukan yan ta’adda ke yin barazanar shigowa ta kananan hukumomin , Shanono ,Bagwai da Tsanyawa domin ba za su bari su shigo ba.

A karshe ya godewa babban sufeton yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, bisa gudunmawar da yake bayarwa babu dare babu rana na ganin an tabbatar da tsaro.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere