Yan Sandan Jihar Neja Sun Bugi Kirjin Sai Sun Ceto Daliban Da Aka Sace

Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.

Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba.

Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban.

Ya kuma ce daga bisani za a ɗauki mataki kan hukumomin makarantar saboda ci gaba da karatu bayan umurnin kulle makarantu a yankin saboda barazanar tsaro.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.