Lauyoyin hukumomin tsaron Najeriya da Sheikh Lawal Triumph ya kai ƙara gaban Babbar Kotun Jihar Kano sun buƙaci a biya su diyyar Naira dubu hamsin (₦50,000) na ɓata lokaci.
A zaman kotun da ya gudana ranar Alhamis, lauyan Sheikh Lawal Triumph, Barista Kabir Yusuf, ya shaida wa kotu cewa sun janye ƙarar da suka shigar, bayan sun zauna da hukumomin tsaro tare da cimma matsaya.
Sai dai lauyan waɗanda aka yi Ƙara, Barista Hashim Hussaini Fagge, ya nemi kotu ta ba da umarni a biya waɗanda yake wakilta ₦50,000 a matsayin diyyar ɓata lokaci, yana mai cewa an gayyaci hukumomi da lauyoyinsu zuwa kotu ba tare da kammala shari’ar ba.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Adamu Abdullahi ya amince da janye ƙarar, tare da yin watsi da buƙatar biyan diyyar Naira dubu hamsin, sannan ya rufe shari’ar gaba ɗaya.
Tun da fari dai, Sheikh Lawal Triumph ya garzaya Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 25, ƙarƙashin Mai shari’a Adamu Abdullahi, inda ya nemi kotu ta hana jami’an tsaro kama shi ko yi masa duk wata barazana.