sojoji

Sojoji Sun Halaka Yan Boko Haram Shida A Borno

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan mayaƙan Boko Haram shida a lokacin da suka daƙile wani hari da mayakan ƙungiyar suka yi yunƙurin kai wa wani sansanin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Cikin wata sanarwa da Laftanar Kalan Sani Uba, jami’in hulda da jama’a na rundunar haɗin kai mai […]

Read more

Sojoji Sun Kashe Yan Boko Haram 15 A Borno

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe mayaƙa sama da 15 a wasu hare-haren da ta kai ta sama a maɓuyarsu da ke dajin Sambisa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ta ce an kai hare-haren ne […]

Read more

Gwamnatin Katsina Tabbatar Da Ceto Mutane 76

Gwamnatin jihar Katsina ta ce sojojin Najeriya sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗanbindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su. A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu’azu ya fitar, ya ce Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau […]

Read more

Sojoji Sun Kama Yan Boko Haram 13 Tare Da Kashe Wasu A Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe kwamandojin ƙungiyar Boko Haram biyu tare da mayaƙa 11 yayin wani artabu na tsawon awanni a jihar Borno. Kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsallam Abubakar yana bayyana Abu Nazir da Abu Fatima a matsayin jagororin da suka yi nasarar kashewa. […]

Read more

Sojojin Najeriya Sun Musanta Miƙa Wuyan Bello Turji

Shelkwatar tsaron Najeriya ta musanta rahotanni da ke cewa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan wanda ya yi ƙaurin suna, Bello Turji ya miƙa wuya ga sojojin ƙasar. Daraktan yaɗa labarai da aikace-aikacen shelkwatar tsaron, Manjo-Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a yau Alhamis. “Maganar ita ce Bello Turji bai […]

Read more

Sojojin Sama Sun Yi Wa Yan Bindiga 400 Luguden Wuta A Zamfara

Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, harin da ta kai ta sama a karkashin rundunar ‘Operation Fansar Yamma’, a ranar Lahadi 10 ga watan Agusta, 2025, ta yi luguden wuta kan taron ‘yan bindiga 400 a lokacin da suke shirin kai hare-hare kan al’ummomi manoma a jihar Zamfara. Kakakin  sojojin, Air Cdre Ehimen Ejodame, […]

Read more

Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga 95 Tare Da Ceto Mutane 138 A Neja

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja. ’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai. Sojoji tare da taimakon jiragen yaƙi na sama sun kai farmaki bayan samun bayanan sirri. Aƙalla ’yan ta’adda 95 […]

Read more