Ba Za Mu Ragawa Tinubu A 2027 Ba-Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce jama’ar Arewacin Najeriya ba za su ragawa shugaba Tinubu ba a zaben 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce jama’ar Arewacin Najeriya ba za su ragawa shugaba Tinubu ba a zaben 2027.
Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe (Grassroot Care and Aid Foundation GCAF) Ambasada Auwalu Muhd Danlarabawa ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karshen yawaitar masu Shaye-Shayen kwayoyi a fadin Najeriya.
A watanni 19 na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a mulkin Najeriya, ƙididdiga ta tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ta gada.
A wata sanarwa da majalsair malaman addinin Musulunci ta Najeriya ta fitar a ranar Litinin 18 ga Nuwamba, 2024, ta bukaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da kudurin yi wa dokar haraji gyaran fuska.
‘Yan Majalisar Wakilai da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna damuwarsu kan wasu kudurori hudu da zasu sake fasalin dokar harajin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ƙarkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na shan caccaka kan kama masu zanga-zangar tsadar rayuwa. Bayyanar faifan bidiyon wasu matasa da a ganin ido basu haura shekara 15 zuwa 20 cikin mummuna yanayi da aka kama sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa ya janyo wa gwamnatin Tinubu tofin Allah ya tsine a kafafen sada zumunta. Faifayin […]
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye ƙudirinsa na ƙara haraji.
Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ake sa ran zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar a kwanakin baya.
Bola Ahmed Tinubu ya wuce birnin Paris na ƙasar Faransa daga birnin Landan na Birtaniya a yau Juma’a.
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugabannin sabuwar Hukumar Raya yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya. Bola Ahmad Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunayen shugabannin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa-maso-yamma domin samun sahalewarsu. Wannan na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta kafa hukumar da shugaban ƙasa ya yi a ranar 24 ga watan […]