Ana Ci Gaba Da Tattara Sakamakon Zaben Gwamna A Anambra

Tuni aka kammala kaɗa ƙuri’a a kusan dukkan rumfunan zaɓen da ke jihar Anambra yayin da sama da mutum miliyan biyu ke zaɓen sabon gwamnan jihar.

Abin da ya rage yanzu shi ne warewa da ƙirga ƙuri’un, wanda shi ma an kammla a wurare da dama.

Hukumar zaɓe Inec na ci gaba da tattara sakamakon a matakin ƙananan hukumomin jihar 21 domin ƙirgawa da sanar da wanda ya yi nasara.

Zuwa yanzu Inec ta wallafa kashi 86.10 cikin 100 na sakamakon zaɓen a shafinta na intanet IReV. Ma’ana ta wallafa sakamako 4,925 cikin jimillar 5,720 da ake buƙata.

Post masu alaƙa

Yar Najeriya ta kammala jami’ar Burtaniya da daraja ta daya (1st Class) a ilimin kimiyar samar da manhajar kasuwancin zamani.

Gwamnati ta buƙaci jama’a su guji taɓa kumfar da ta ɓulla a hanyar Kaduna-Abuja

A riƙa yi wa masu shirin aure gwajin miyagun ƙwayoyi :- Buba Marwa