Charles Soludo Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Anambra

Hukumar zaɓen mai zaman kanta INEC ta sanar da Charles Soludo na Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda aka yi a jiya Asabar, 8 ga watan Nuwamba.

Baturen zaɓen jihar, Farfesa Edoma Omoregie ne ya sanar da sakamakon a cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke babban birnin jihar, Awka a safiyar yau Lahadi.

Ya ce Soludo ya samu ƙuri’a 422,664, sai kuma Nichola Ukachukwu na Jam’iyyar APC mai biye masa da ƙuri’a 99,445.

George Moghalu na Jam’iyyar Labour ne ya zo na uku da ƙuri’a 10,576, sai Jude Ezenwafor na PDP mai ƙuri’a 1401.

Charles Soludo wanda tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne, ya lashe zaɓen ne domin yin sake mulkin jihar a karo na biyu.

Post masu alaƙa

2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa

2027: NDC ta zargi APC da gwamnatin Kano da shirin yin magudi ta tsarin tattara sakamakon zabe na INEC

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano