NOA da INEC sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa gabanin zaɓen 2027

 

Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa, wato NOA, da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, sun bayyana aniyarsu ta ƙara haɗa kai domin wayar da kan al’umma kan yadda ake zaɓe da kuma muhimmancin fitowa domin kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen shekarar 2027.

Babban Daraktan Hukumar NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar girmamawa ga Shugaban Hukumar INEC a Abuja.

Ya ce dimokuraɗiyya ba za ta yi ƙarfi ba sai idan jama’a sun fahimci yadda tsarin zaɓe yake gudana, kuma suka fito suka yi amfani da haƙƙinsu na zaɓen shugabannin da suke so.

A cewarsa, zaɓen shekarar 2023 ya nuna cewa mutane da dama, musamman waɗanda suka yi zaɓe a karon farko, ba su da cikakkiyar masaniya kan tsarin zaɓe. Wannan kuma ya sa aka samu yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma ruɗani a tsakanin jama’a.

Mallam Issa-Onilu ya ce NOA na da ofisoshi a dukkan jihohi da ƙananan hukumomi na ƙasar nan, don haka za ta iya isar da saƙon wayar da kai zuwa kowane lungu da saƙo na Najeriya.

Ya ƙara da cewa aikin hukumar ba wai bayyana shirye-shiryen gwamnati kaɗai ba ne, har ma da koyar da kishin ƙasa da ƙarfafa mutane su kula da dukiyoyin gwamnati. Ya ce idan gwamnati ta gina amincewa tsakanin ta da jama’a, mutane za su fi son ƙasarsu kuma su kare dukiyarta.

Daga cikin shawarwarin da NOA ta gabatar wa INEC akwai a riƙa wayar da kan masu zaɓe a kodayaushe, ba sai lokacin zaɓe ya gabato ba. Haka kuma ta buƙaci hukumomin biyu su riƙa gudanar da shirye-shiryen wayar da kai tare.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar INEC ya ce wannan haɗin gwiwa yana da matuƙar muhimmanci, domin ba za a samu ingantaccen zaɓe ba idan jama’a ba su fahimci darajar ƙuri’arsu ba.

Ya ce duk da ci gaban da aka samu wajen amfani da na’urori da fasaha a zaɓe, har yanzu rashin fitowar jama’a zaɓe, yaɗuwar labaran ƙarya da kuma sayen ƙuri’u na ci gaba da zama babban ƙalubale.

Shugaban na INEC ya yi kira ga hukumomin biyu da su fara shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027 tun daga yanzu, ta hanyar ƙara wayar da kan jama’a da kuma yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya da sayen ƙuri’u.

Dukkan hukumomin biyu sun bayyana cewa suna sa ran wannan haɗin gwiwa zai ƙara yawan masu fitowa zaɓe, ya ƙarfafa wayar da kan jama’a, tare da inganta sahihancin zaɓe a Najeriya.

Post masu alaƙa

Harin Lassa: Zulum ya tura tawaga ta musamman yankin, an rufe wasu makarantu

Mutanen gari sun fatattaki ’yan bindiga tare da kashe 4 daga cikinsu a Katsina

Zargin juyin mulki: DSS ta kama mutum 5 na hannun daman Sylva