An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi a Kano

Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano sun nuna cewa an samu ƙarancin fitowar mutane zaɓukan cike gurbin wasu ƴan majalisar dokokin jihar biyu.

An gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓe 1,014 a faɗin ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal.

Bayanai sun nuna cewa duk da isar jami’an zaɓe rumfunan a kan lokaci, da dama mutane sun ƙi fita zaɓukan.

Hukumar zaɓen ƙasar dai ba ta saka sunan jam’iyyar NNPP da ADC da PDP a kan takardar kaɗa ƙuri’a ba.

Kawo yanzu dai babu rahoton wani tashin hankali a zaɓukan.

Jami’an tsaro sun ƙarfafa tsaro a wuraren da ake gudanar da zaɓukan

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Kotu ta soke nasarar ɗan takarar ADC a Majalisar Wakilai