Zaɓen cike gurbi: Rundunar ƴan Sandan jihar Kano ta taƙaita zirga-zirga a Dawakin Kudu da Warawa.

CP IBRAHIM ADAMU BAKORI

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bayyana matakan tsaro da aka amince da su gabanin zaben cike gurbin ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa wanda zai gudana ranar Asabar.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar,CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar

Yace bisa umarnin kwamishinan yan sandan jihar Kano,  CP Ibrahim Adamu Bakori , an takaita zirga-zirga a yankunan da za a gudanar da zaben daga karfe 12:00am na daren juma’a  zuwa ƙarfe 5:00pm na yammacin ranar Asabar, sai dai dokar ba ta shafi masu gudanar da aiyuka na musamman ba.

Ya ce an tura isassun jami’an tsaro yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da sanya idanu kan yadda zaben zai gudana.

Sanarwar ta bukaci masu zabe su fito cikin lumana domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Rundunar ta bayyana cewa ba za ta lamunci tashin hankalin zaɓe, siya ko sayar da ƙuri’a, kwace akwatunan zaɓe, tsoratar da masu zaɓe, da kuma yaɗa labarai na ƙarya ba.

Duk wanda aka samu yana aikata wani nau’in magudin zaɓe za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu bisa ga dokar Zaɓe ta shekarar 2022.

Post masu alaƙa

Tinubu ya tura Shettima ya wakilci Najeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka

APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai

NAHCON ta musanta zargin karkatar da kujerun Hajjin 2027