Takutaha: ‘Yan sanda sun kama mutane 29 da makamai da kayan maye

Rundunar ƴan sandan Jihar nan ta ce ta kama mutane 29 ɗauke da makamai da kayan maye a lokacin bikin Takutaha da aka yi a fadin birnin.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama mutanen ne a wurare daba-daban a faɗin jihar nan.

A cikin bidiyon da Kiyawa ya yi bayani an ga makaman da rundunar ta baje a gaban wadanda aka kama a hedikwatar ƴan sanda dake Bompai.

Makaman sun haɗa da wuƙaƙe da almakashi da ɗan bida da adduna, haka kuma an kama tabar wiwi, kamar yadda SP Kiyawa ya bayyana a ƙarshen mako.

Post masu alaƙa

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP