‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto

Wani rahoto da hukumar ƙididdigar jihar Sokoto ta fitar ya nuna cewa yanzu haka girman talaucin ya faɗo ƙasa warwas daga kaso 91 zuwa 41.

Rahoton ya alƙanta cigaban da aka samu da irin ƙokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen inganta rayuwar al’ummar karkara, inda a shekarar 2026 gwamnatin ta ware kaso 70 na kasafin kuɗinta ga fannin samar da kayan more rayuwa.

Rahoton ya alaƙantatalauci da matsalar tsaro, inda al’amarin ya fi ƙamari a wasu ƙananan hukumomi kamar Tangaza da Binji wadanda ke fama da matsalar tsaro.

A 2022 dai rahotanni sun nuna girman talauci a tsakanin al’ummar jihar ta Sokoto, inda ya kai kaso 91, abin da ya sanya jihar ta Sokoto a jerin jihohin da suke kan gaba a fannin talauci.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun