Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sanya hannu kan doka kafa kotuna na musamman domin gaggauta yanke hukunci ga ’yan ta’adda, ’yan fashi da makami da sauran masu laifi a fadin jihar.
Wannan doka na da nufin kawar da dukkan ayyukan assha da suka haɗa da fashi, ƙwacen waya, da rikice-rikice a cikin al’umma, waɗanda ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
Gwamna Radda ya ce gwamnati ba za ta lamunci aikata laifuka ba, musamman waɗanda ke iya janyo mutuwa kamar yadda ya faru da wani Abu Amshi da aka kashe saboda rikicin ’yan daba. Ya jaddada cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A taron tsaro da aka gudanar tare da manyan jami’an tsaro, Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnati ta yi amfani da sashe na 5(2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara) domin kafa irin wannan doka.
Ya ce: “Saboda haka gwamnati ta sanar da kafa kotun tafi da gidan ka domin hanzarta yanke hukunci ga duk wanda aka samu da laifi.”
Taron ya haɗa jami’an tsaro daga ’yan sanda, DSS, Sibil Difens, Hukumar NDLEA, Hisba, shugabannin ƙananan hukumomi, da sauran hukumomi, tare da Kwamishinan Shari’a da muƙarraban gwamnati. An bayyana cewa dokar za ta fara aiki ba da jimawa ba.
Wani mazaunin jihar, Alhaji Maiwada ya ce: “Tuni ya kamata a yi wannan doka. Idan muka tuna da lokacin mulkin Shema, duk wanda aka kama da laifin ƙauraye ana kiran sa da ɓarawo, duk da munin aikin sata.”
Shi kuwa Malam Sabi’u ya yi nuni da cewa muƙarraban gwamnati, musamman ’yan siyasa, su ne ya kamata su fara bin wannan doka tare da tilasta wa magoya bayansu bin ta.
Ya ce: “Yawancin masu irin wannan aiki ’yan bangar siyasa ne, waɗanda ake ba su ƙwayoyi don su yi tallata nasu ko kuma su yi wa abokan hamayya rashin kunya. Idan babu abin sha, sai su koma ƙwace ko rikici.”