Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi lamarin da ta ce ya haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar mai lura da shiyyar birnin tarayya Abuja da Kogi, Godfrey Aba ya tabbatarwa da manema labarai kan cewa ƙungiyar za ta shiga yajin aikin ne daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni, matuƙar gwamnatin ƙasar nan ba ta janye matakin cire tallafin man ba.
Ya ƙara da cewa ”ƙungiyar za ta shiga yajin aikin ne har sai gwamnati ta janye matakin da ta ɗauka”.
Wannan saƙo ya fito ne daga muƙaddashin sakataren ƙungiyar na ƙasar Dominic Igwebike, wacce ta yi kira ga mambobinta da su yi biyya ga matakin ƙungiyar na tsunduma yajin aiki a tsakiyar makon mai zuwa.