Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya cigaba da abin da ya yi alkawari na karbe filaye gwamnati da aka yi gine-gine a kan su. A daren Lahadin nan, labari ya zo daga gidan rediyon Freedom cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ruguza gini da aka yi a otel da ake kira da Daula.
Sabon Gwamnan ya na ikirarin an yi wadannan gine-gine ne ba a kan ka’ida ba, don haka tun kafin ya dare kan kujera, ya sha alwashin kai su kasa
Tun a ranar Asabar, sabon Gwamnan ya bada umarnin rusa duk ginin da ya sabawa ka’idar jiha.
Kamar yadda sakataren yada labaran na gwamna Sanusi bature Dawin-Tofa ya fitar,inda yace, gwamnati ba za ta yarda da gini a makarantu, kasuwanni, asibitoci da duk wuraren al’umma ba domin yin hakan zai dawo da kimar jihar sannan zai tabbatar da tsari tare da kawata wuri da inganta tsaro.
A gefe guda, wannan ya jawo surutu daga wasu mutane da suke ganin an jawowa jama’a asara.