A yau Laraba 4 ga ‘ Satumbar 2024 ne aka ƙaddamar da taron ƙungiyar tuntuɓa ta Arewacin Najeriya a hedikwatar ƙungiyar da ke jihar Kaduna.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga yankin, daga cikin dattawan Arewacin Najeriya da ke zaune a ɗakin taron akwai tsofaffin gwamnoni, sarakuna , shuwagabannin tsaro da jigajigan ‘yan siyasa.
A ɗakin taron akwai tsofaffin gwamnonin jihar Kano guda biyu Sanata Kabiru Gaya da Sanata Malam Ibrahim Shekarau, da kuma tsofaffin gwamnonin jihar Jigawa Sanata Saminu Turai da kuma Alhaji Sule Lamiɗo.
Daga jihar Nasarawa akwai tsofaffin gwamnoni guda biyu Alhaji Abdullahi Adamu da kuma Tanko Almakura.
Akwai tsofaffin gwamnonin jihar Bauchi guda biyu Barista Mohammed Abdullahi da kuma Alhaji Ahmad Mu’azu.
Daga cikin manyan jami’an tsaron Najeriya akwai Tsohon shugaban Hukumar shigi da fice ta Najeriya Muhammad Babandede.
, tsohon kakakin rundunar sojojin Najeriya Sani Usman kuka sheka, tsohon shugaban Rundunar ‘yan sanda MD Abubakar.
An samu halartar manyan malaman addinin Musulunci da na boko, sarakunan gargajiya daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya