Tinubu ya cire ministan kuɗi da na gidaje

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wasu sauye-sauye a majalisar ministocin ƙasar, inda ya cire ministan kuɗi, Wale Edun da ministan gidaje, Ahmed Musa Dangiwa.

A wata sanarwa da sakataren gwamnatin ƙasar, Sanata George Akume ya fitar, ya ce an buƙaci ministan kuɗin ya miƙa aiki ga ƙaramin ministan kuɗin ƙasar, Taiwo Oyedele, wanda zai maye gurbinsa a matsayin sabon babban ministan kuɗin sannan kuma mai jagorantar harkokin tattalin arzikin ƙasar.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu ya naɗa Muttaqa Rabe Darma a matsayin sabon ministan gidaje, a yayin da aka buƙaci Dangiwa ya miƙa aiki ga ƙaramin ministan ma’aikatar na wucin-gadi.

Bugu da ƙari, sanarwar ta buƙaci a miƙa aikin daga yau Talata zuwa ranar Alhamis, 23 ga watan Afirlun.

Shugaba Tinubu ya yi godiya ga tsofaffin ministocin, sannan ya musu fatan alheri a ayyukansu na gaba.

Post masu alaƙa

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC