An tsinci gawar matashi a kusa Asibitin Mallam Aminu Kano.

An tsinci gawar wani matashi mai suna, Aliyu Mustapha, a cikin Kwalabatin kusa da asibitin Mallam Aminu Kano.

Mijin ƙanwar mahaifiyar marigayin, Malam Salisu, ya bayyana cewa makonni biyu kenan suke nemansa amma basu ganshi ba,inda lamarin ya tayar mu su da hankali.

Sai dai ya ce daman bashi da lafiya zazzaɓi ne yake damunsa, kuma sun kai shi asibitin koyar na Mallam Aminu Kano, don duba lafiyarsa, inda ya fito ba tare da saninsu ba, kuma lokacin da akaga gawar tasa akwai wayarsa ƙirar Iphone 17 a cikin Aljihunsa.

Ya ƙara da cewa zuwa yanzu basa zargin kowa, sai dai kawai bincike ne zai tabbatar da abunda da ya faru, domin tun a ranar 9 ga watan Afrilun 2026 ya fito daga asibitin.

Wasu shaidu sun tabbatar da cewa mahaifiyar marigayin ce ta ce jinyarsa, lokacin da lamarin ya faru.

Tuni jami’an ƴan sanda suka ɗauke gawar tare da miƙa ta zuwa asibitin Mallam Aminu Kano.

Post masu alaƙa

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa

Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.